[Android] Yadda ake gyara matsalar (There was a problem parsing the package) A wayar Android - Jarida24
Welcome To Jarida24.com.ng - Best Tech site & Solution, App Download For Free...

recent

[Android] Yadda ake gyara matsalar (There was a problem parsing the package) A wayar Android



Assalamu Alaikum barkanku da wannan lokaci,
to kamar de yanda na Alkawar ta muku kan
cewa zanyi muku bayani na yanda ake gyara
matsalar (There was a problem parsing the
package) to insha Allah yanzu zamu tsunduma
cikin bayani
.
To kamar de yanda kuka sani irin wannan
matsalolin suna faruwa a wayoyin android
yayin da za,ayi install na wani apps ko games
din, wani lokacin sai an turoma da wani apps
ko games kokuma kayi download dinsa to da
zarar kazo zaka budeshi sai yakiyin install
saiya Rubuta (There was a problem parsing the
package) kana gani dole saide ka hakura ka
gogeshi sakamakon Rashin sanin yanda
za,kayi, to idan kunga irin wannan matsalar ya
faru to app ko game dinne bana wayarba wato
yayi mata kadan kokuma yayi mata girma.
Yawancin app din da zakuga hakan to Android
minSdk version da targetSdk version din sane
baizo dede dana wayar takaba sabi da kowane
waya yana tana dauke da nata idan kaga app
ya baka wannan matsalar to wannan app din
version dinba da bambanci dana wayar taka
amma ba version na ainihin wayawa wani
version ne mai sune API idan kaga hakan to
sune basuzo dedeba shiyasa wannan app ko
game yake nuna (There was a problem parsing
the package) domin kowace waya da nata API
Level din. Sabo da haka insha Allah yanzu zan
muku bayanin yanda zaku gyara irin wannan
matsalar, abin da ake bukata kawai nutsuwa
sabi da haka inde zaka nutsu to Insha Allah
zakayi nasara
.
Da farko abin da ake bukata sune:
.
Kuyi Download na "Apk Editor pro" saiku shiga
nan domin ku daukota Download apk editor-pro
.
Sannan kuyi download na "CPU-Z" shima ku
danna nan ku dauko Download CPU-Z
.
Kokuma ku daukosu a google kokuma a play
store
.
Bayan kun saukar da wadannan applications
din to yanzu saikuyi install dinsu
.
Bayan kunyi install to saiku fara bude "CPU-Z"
shi wannan application amfaninsa shine
bayyana gaskiyar dukkan abubuwan da suka
kunshi wayarka kamar model, version, screen
size, ram, API Level, da sauran abubuwa da
suka shafi kwakwalwar wayarka, to misali idan
muka dauki "API Level" to shi wannan shine
version na application da zaiyiwa wayarka
kuma kowace waya tana da nata "API" to idan
kukaga app/game yakiyi yana nuna (There was
a problem parsing the package) to wannan API
dinne na wayar taka baizo dede dana app din
dayaki yiba sabi da haka yanzu bayan kunyi
install din CPU-Z din saiku budeshi idan kun
bude zakuga Rubutu a sama kamar haka:
.
80, DEVICE. SYSTEM, BATTERY,
da sauransu
.
To kawai saiku shiga "SYSTEM" da zarar kun
shiga zai budo muku wani shafi to saiku duba
anan xakuga API Level din wayar taku sai kuyi
copy dinsa kokuma ince ku haddacesu domin
guda biyune kacal zamuzo kansu nan gaba
wato zamu gaya muku inda ake amfani dasu

To bayan kun gano API din wayar taku to saiku
fito daga cikin wannan app din yanzu saiku
koma ku bude "Apk editor pro" idan ya bude ku
shiga inda aka Rubuta "Select an Apk File"

idan kun shiga zai kawoku cikin file manager
dinku to sai kuje inda wannan app ko game din
yake sai kuyi click akansa


da zarar kun danna akansa zakuga ya kawo
muku wani Rubutu to saiku shiga inda aka
Rubuta "Full Edit (RESOURE RE-BULD)"

Da zarar kun shiga zakuga ya kawoku wani
shafi to saiku duba kasa daga gefan dama
zakuga inda aka Rubuta "Manifest" to saiku
shiga nan

Da zarar kun shiga nan zakuga ya kawoku
Manifest na app din zakuga wasu tarkacen
Rubutu to wannan tarkacen sune code na app
din kowane app ko game yana da wannan
domin da sune aka hada kowane irin app/game
kuma kowanne nasa dabam. To wannan
Rubutun da kuka gani ajere to saiku shiga
wanda zaku ganshi kamar haka:
.
< uses-sdk androidminSdkversion ="21" . Ko
makamancin hakan,

da zarar kun shiga zai bude muku wani shafi
wanda zakuga wasu numbobi misali
.
android minsdkversion
21
.
android tagetsdkversion
22

To wadannan lambobi da kuka gani 21 da 22
sune Minsdk da tagetsdk kowane applicaton ko
games yana da nasa lambobin sannan zaku iya
ganin wasu lambobin bawai dole sai wanda na
bada misalina to idan kunga app/game yakiyi
to wannan lambobin sune basuzo dede dana
wayar takuba shiyasa app/game din yake
Rubuto (There was a problem parsing the
package) yayin da kazo install sabi da haka
dole sai an chanjasu zuwa na wayar sannan
app din zai samu damar yi, kuma kamar yanda
na gaya muku kowace waya da nata, idan baku
mantaba a farko munyi muku bayanin yanda
zaku gano API din naku wanda nace ku gane
lambobin zamuzo kansu nan gaba sabo da
haka yanzu munzo kansu dan haka wannan API
din na wayar taka daka gano sune zaka cire
wadanan
.
android minsdkversion
21
.
android tagetsdkversion
22
ka sanyasu wato ka cire 21 da 22 dinnan ka
sanya wanda ka gano ta cikin CPU-Z dinnan
wato API Level dinnan. Da zarar ka chanja
shikkenan saika danna save bayan ka danna
zakaga ta dawo dakai shafin to karka damu ka
duba sama daga gefan dama zakaga inda aka
Rubuta "BUILD" to saika dannan

Da zarar ka danna zakaga ya fara build din
saika dan jira kadan har saiya gama da zarar
ya gama sai nunama Install da kuma close to
sai ka danna Install, nan take zakaga ya
farayin install
.
Shikkenan kayi maganin wannan matsalar
kuma duk lokacin da irin hakan ya faru sai abi
wannan hanyar insha Allah za,ayi nasara
.

Drop Your Comment

0 Comments