An Lalata Magungunan Da Suka Gama Aiki na Naira Miliyan 15 A Jihar Ekiti - Jarida24
Welcome To Jarida24.com.ng - Best Tech site & Solution, App Download For Free...

recent

An Lalata Magungunan Da Suka Gama Aiki na Naira Miliyan 15 A Jihar Ekiti

Gwamnatin jihar Ekit ta lalata magungunan da
suka kai Naira miliyani 15, wadanda aka kwato su
daga asibitocin al’umma a duk fadin jihar.
Sakataren dindindin na ma’aikatar lafiya Dokta
Ayotunde Omole shi ne wanda ya wakilci gwaman
jihar jihar shi ne wanda ya wakilci gwamnan jihar
Kayode Fayemi, wanda kuma shine ya shagabnci
konawa da kuma lalata magungunan da a Ilokun
Dumpsite cikin Ado Ekiti,babban birnin jihar, ya
bayyana cewar shi abin da aka yi ya zamma dole
ne, saboda a raba ita jihar da magunguna masu
hadari.
Fayemi ya ci gaba da cewar shi matakin daya
dauka zai ba mulkin shi wata dama ta, kawo gyara
a bangaren lafiya, duk irin yadda yake so, da
kuma samarwa al’ummar jihar magunguna m,asu
inganci. “ Shi al’amarin lalata magungunan zai
tabbatar da cewar mutane wadanda basu da hali
mai kyau , ba a basu dama ba, wajen da za su
samu damar amfani da magungunan da suka
gama aiki ba, wajen yi ma mutane allura, suna
kasancewa cikinal’umma ba.”
Gwaman ya cin gaba da bayanin cewar alamun
magungunan da amfanin su ya kare, sun hada da
za su kasance ba su da nagarta zuwa wani lokaci
ya kuma kasance nau’in su ya canza kala,saboda
dadewar daka yi ana ajiyar shi, har dai ya kai ga
kasancewa abin da zai iya zama guba, a dalilin
wata matsalar da aka samu.
Da yake yi ma ‘yan jarida jawabi a wurin Omole ya
bayyana cewar, magunguna da suka gama aiki
suna iya lalata wasu wurare cikin jiki, sui sa a
kasa zaune a kuma kasa tsaye, da kuma
abubuwan da suka iya faruwa nna gaggawa.” Wani
babban hadarin daya ke tattare da shan
magungunan da amfanin su ya kare, shin yasa ita
gwamnatin jihar Ekiti, ta sanar da duk wasu masu
aka shiga dukkan manya da kuma kananan
asibitocin da suke jihar saboda ayi hakan da a
kwashe dukkan irin magunan da suka kare
amfania lalata su”.
Babban jami’a ta wurin da ake ajiye magunguna
Mrs Olabisi Arogundade ta bayyana cewar, an yi
irin wannan al’amarin na kona magungunan da
aikin su ya kare cikin shekarars 2008, dun daga
wancan lokacin ne aka kwashe duk irin
magungunan da aikin suka kare daga asbitoci .

Drop Your Comment

0 Comments