[Android] Yadda ake gyara matsalar wayar android yayin da kayi Restore, sai wayar ta nuna sai ansa email kuma ko ansa email din ba zata yiba har sai anyi mata flashing - Jarida24
Welcome To Jarida24.com.ng - Best Tech site & Solution, App Download For Free...

recent

[Android] Yadda ake gyara matsalar wayar android yayin da kayi Restore, sai wayar ta nuna sai ansa email kuma ko ansa email din ba zata yiba har sai anyi mata flashing


Barkanmu da wannan lokaci, kamar de yanda
na Alkawar ta muku kan cewa zan koyar daku
yanda ake magance irin wannan matsalar
batare daka kaita wajen masu flashing ba, sabo
da haka da fatan kun shirya tsaf domin ganin
yanda zakuyi,
.
Mutane dayawa suna fuskantar irin wannan
matsalar musamman masu amfani da wayar
android kamar su Tecno, Gionee, Samsung,
Lenevo, Itel da sauransu, misali idan muka
dauki tecno kamar W2 W3 W5 zakuga wani
lokacin idan kukayiwa wayar Restore to zakuga
kawai ta dawo muku da wannan matsalar haka
kawai dagayin Restore idan ka gama Restore
din kawai saita kawoka wani shafi dabam da
zata cema dole saika sanya email, kuma wani
lokacin koda ka sanya email din sai kaga taki
budewa, wani kuma baimasan email dinba balle
yasa, wasu wayoyin kuma irin wannan
matsalolin suna faruwane yayin daka antaya
wayarka a double click wato dole sai an ta6a
sau biyu sannan ta shiga kokuma ka laftata a
touch & spech wato ka sanyata tana magana,
to yayin daka antaya wayarka a irin wannan
chakwalkwalin to misali ka sanyata tana
magana duk inda ka shiga tana fadin inda ka
shiga, to idan ka maida wayarka hakan to
zakaga ta koma double click kokuma kaga tana
dan kakkamewa, to kai kuma hakan saiya
hanaka sakat sabi da kafin ka shiga wani gun
bata lokacine, to yayin daka yiwa wayar
Restore, to shikkenan idan ta bude zakaga ta
umarceka da kasanya email to kaikuma baka
da email din kokuma bakasan ainihin email
dinba karshe dole sai kaje wajen masu flash ka
biya kudi sannan a gyarama, sabo da haka
daga yanxu insha Allah da kanka zaka gyara
batare da Computer ba ko wani software.
.
To a gaskiya yawancin kowane waya akwai
yanda ake gyara irin nata misali tecno akwai
yanda zakuyi nata haka gionee da sauran
wayoyi dan haka wannan hanyar dazan bayar
tana iyayi a wasu wayoyin musamman tecno
da gionee dan haka kowa saiya gwada
akowace irin waya idan tayi shikkenan idan
kuma ka gwada batayiba to saiku ajiye mana
comment da sunan wayarku zamu tura muku
na yanda zaku yiwa irin wayar taku,
.
Yauwa to da farko ku tabbata wayar taku
akwai change kada yayi kasa da 50% sannan
kuma ku tabbata inda kuke akwai Wifi idanma
babu to zaku iya connecting dana wata wayar
dabam, wato idan zakuyi dole zaku nemo wata
wayar dabam wanda akwai data acikinta to
idan kun nemo wannan wayar to sai kuyi create
na hotspot acikinta, wato kuje setting saiku
shiga "more" zakuga inda aka Rubuta
"Tethering & portable hotspot" idan ya bude sai
kuyi on na "wifi hotspot" sannan ku shiga "Set
up Wi-Fi hotspot" idan ya bude zakuga
"Network SSID" saiku sanna sunanku kokuma
wani sunan dakuka gadama sannan a kasa
zakuga inda aka Rubuta "Security" saiku
dannan saiku zabi "WPA PSK" saiku danna
sannan akasa zakuga inda aka Rubta
"password" to saiku sanya password din da
kuka gadama amma ya kasance daga guda
takwas zuwa sama kar yayi kasa da guda 8,
idan kun gama sai kuyi save shikkenan kunyi
create na wifi a wannan wayar,
.
To yanzu kawai saiku dauko wayar taku wanda
zaku gyara matsalar sa email din saiku
kunnata to da zarar ta gama kunnuwa zata
kawoku zata nuno muku "Welcome" ku duba
kasa zakuga wani dan cycle yellow saiku ta6a
nan da zarar kun ta6a zata kawoku wani shafi
wanda daga sama ana Rubutua "Insert SIM
card" to saiku duba kasa daga gefan dama
zakuga inda aka Rubuta "Skip" saiku danna nan
da zarar kun danna zai budo muku wani shafi
wanda aka Rubuta " Did you know your phone
can use Wifi-Fi for calls" karka damu kawai ka
danna inda aka Rubuta "SKIP" to da zarar ka
danna zakaga ya kawoma wifi wanda suke a
kunne to anan zakaga ya kawoma wifi na
wannan wayar wanda kayi create na wifi, da
zarar ya nunoma sunan daka sanya awancan
wifi na wancan wayar to saika danna kan
sunan daya nemo, da zarar ka danna zai
nunama kasa password to anan ma saika
sanya password din dakayi create din wanda
nace karka sanya kasa da guda 8, to da zarar
ka sanya password saika duba daga kasan
inda kasa zakaga "CONNECT" saika danna nan
da zarar ka danna shikkenan kayi connect da
wifi din to da zarar ka gama connect zakaga ta
kawoka wani shafi dabam wanda aka Rubuta
"Checking connection" saika dan jira kadan
zakaga ta nuno "Software update" nanma saika
dan sake jira idan ta gama zata nuno
"Checking inpo..." nan ma ka jira da zarar ta
gama zakaga ta dawo dakai wajen da zakasa
email, to karka damu kawai ka shiga "Enter
your email" saika yi Rubutu a wajen karka
damu ba dole sai email ba ko wani abunne
kadan Rubuta kamar harafi 7 zuwa 10 bayan ka
danyi wannan Rubutun a wajen to kawai sai
kayi long press akan wannan Rubutun daka
Rubuta wato ka danne Rubutun har sai kaga
yayi mark wato har sai wani shudin abu ya
rufe Rubutun, to bayan kayi mark na Rubutun
to saika dan danne wanna alamar ta kasan
wannan kifiyar da ake mayar da Rubutu
manyan baki idan kadan danneta saika dan
jata zuwa sama zuwa alamar mayar da manya
bakin, to da zarar kayi haka zakaga ta kawoka
google to karka damu kawai ka ta6a sama
wajen search saika goge Rubutun dayake ciki
saika Rubuta "setting" kaga Rubuta setting din
zakaga setting na wayarka ya bayyana to karka
damu kawai ka shiga idan ya bude saika je
wajen yin Restore wato "Backup & Restore"
shikkenan sai kayi Restore na wayar da zarar
ta gama Restore din shikkenan zakaga ta bude
nomal shikkenan kayi maganin wannan
matsalar,
.
To amma wata wayar bata daukan wannan
hanyar, wato ba ,a danne wannan alamar da
kuma wajen mayar da Rubutu manya, to idan
ka gwada bai yiba to saika gwada wannan,
bayan ka kamma komi ta nunoma wajen sa
email to saika danyi Rubutu a wajen enter your
email kadanyi kowane irin rubutu, idan kayi
Rubutun sai kayi mark dinsa idan kayi mark din
zakaga wani rubutu ya fito kamar copy cut da
kuma wata alamar kamar haka : kokuma ... To
saika taba wannan alamar zakaga ta nuno ma
"share" to saika danna idan ka danna zata
nunoma wasu apps zakaga Gmail to saika
danne shi har sai ya kaika App inpo idan ya
kawoka nan saika shiga "Notification" idan ya
bude saika shiga inda aka Rubuta "App
Settings" da zarar ya bude saika shiga wannan
alamar ta : kokuma ... A zaye daga sama a
gefan dama da zarar ka danna nan saika shiga
inda aka Rubuta "Manage Account" saika
danna continue kana danna wa zai kawoka
"Setting" na wayarka to sai kaje Backup &
Restore sai kayi shikkenan
.
Wasu wayoyin kuma da zarar ta nunoma wajen
enter your email to saika danyi Rubutu a wajen
sannan kayi mark dinsa da zarar kayi mark
saika dan danne alamar @ Idan kadan danne
alamar @ din saika dan ja kadan nan take
zakaga ta kawoka google search to saika
Rubuta Setting anan zakaga setting na wayarka
ya bayyana shikkenan saika shiga kaje kayi
Restore,
.
Wasu wayoyin kuma bayan kayi connecting na
wifi saika dinga yin back har saika dawo shafin
farko wanda aka Rubuta "Welcome" idan ka
dawo wannan shafin to kawai saika danna
"Minimize" na wayarka da zarar ka danne
zakaga ta nunama dukka minize dinka to karka
damu ka duba daga sama zakaga wajen search
wato Google search keybord nakan wayarka to
kawai saika shiga nan zai tambayeka to kawai
ka danna inda aka Rubuta No thank idanma bai
tambaya shikkenan kawai inya bude zakaga
wajen rubutu to kawai saika Rubuta Setting da
zarar ka rubuta nan take zai kawoka zuwa
setting na kan wayarka shikkenan saika shiga
kaje kayi Restore na wayar shikkenan kayi
maganin wannan matsalar
.
Wadannan sune kadan daga cikin hanyoyin
magance irin wannan matsalar, kamar de
yanda tun a farko na gaya muku kan cewa ba
kowace wayace take daukan irin wadannan
hanyoyinba yawancin kowane waya da yanda
akeyin nasa dan haka saide ku gwada idan
baiyi a wayar kuba to zaku iya ajiye mana
comment da sunan wayar taku saimu gaya
muku na yanda zakuyi irin wayar taku
.
Kuma insha Allah anan gaba zamu dinga kawo
muku videos kala kala na yanda akeyiwa
wayoyi dabam dabam kude karku damu kawai
kuci gaba da ziyartar wannan shafi akoda
yaushe
.
Idan akwai mai tambaya sai yayi comment

Drop Your Comment

0 Comments