[Android] YADDA ZAKA YIWA ABOKINKA CHAJIN WAYARSA DA WAYAR ANDROID - Jarida24
Welcome To Jarida24.com.ng - Best Tech site & Solution, App Download For Free...

recent

[Android] YADDA ZAKA YIWA ABOKINKA CHAJIN WAYARSA DA WAYAR ANDROID


Wasu lokutan kaida abokinka kunaso kuyi turi
na wani abu a tsakaninku sai kuma kaga an
samu matsala babu chaji a wayar shi abokin
naka wanda zaima turin kai kuma abun kana
bukatarsa da gaggawa amma dole ka hakura
sabo da matsalar rashin chaji a wayar wannan
abokin naka gashi kuma babu wani hanyar
chaji a wannan lokacin,
To Alhamdulillah a yanzu insha Allah inde irin
wannan matsala ya faru to cikin sauki zaka
chaja wayar abokin naka. Ga yadda zakuyi idan
hakan ta faru,
Da farko ka samu { OTG cable } shi otg cable
wani cable ne na zamani wanda wasu wayoyin
zakuga suna zuwa dasu wato cable ne zaku
ganshi da kai guda biyu wato dana chaja
android da kuma usb to irin wannan shine otg
cable zaku iya samunsa a shagunan da akese
da kayayakin waya, to da zarar kun samu
wannan cable din to shikkenan duk lokacin da
irin haka ya faru cikin sauki zaku jonawa
abokinku ku bashi chaji, to da zarar kun nemo
wannan otg cable din saiku jona wajen charge
din ajikin taku wayar sannan kayi connect din
wayar da zaka baya chargin din, bayan hayi
haka shikkenan, nan take daya wayar wanda
bata da charjin zatana zukar na daya wayar
mai chargin shikkenan ka yiwa abokinka chargi,
ammafa ka sani ita wayar abokin naka a
gaskiya bazata cikaba misali idan mai chargin
tana da 100% to wanda ka jonawan da zarar ta
kai 70% ko 80% zata dena zuka shaka abun
yake, sannan kuma ka sani shi irin wannan
cable din baya aiki a wayoyi tsofin yayi wanda
ta jima saide wayoyinmu na yanzu dan haka
saide ka gwada idan zaiyi a taka, Allah ya bada
sa,a

Drop Your Comment

0 Comments