Yanda Ake Cirema Memory Card Password A Wayar Andriod - Jarida24
Welcome To Jarida24.com.ng - Best Tech site & Solution, App Download For Free...

recent

Yanda Ake Cirema Memory Card Password A Wayar Andriod

A yau insha Allah zamuyi bayani ne game da
Yadda ake Cirema Memory Card Password
A Wayar Android, batare da anje gun masu
computer ba, sau da dama mutum yakan
manta password din memory card nasa, toh in
kana daya daga cikin mai fuskantar wannan
mastala ci gaba da karanta wannan darasi
domin zai taimakeka/ki.
Hanya mafi sauri da kuma sauqi sosai,
shine yin hikima ta hanyar amfani da
application mai suna ES File Explorer a
wayar Andriod.
Domin yin haka kawai kubi wadannan
hanyoyi kamar haka;
1. Da farko kawai kasa Memory Card din
da yake da Password din a cikin wayar
Andriod
2. Saika bude wancan application mai
suna ES File Explorer idan kuma baku
dashi sai ku sauke shi ta Google.
3. Saika duba folder mai suna mmcstore
4. Saikayi rename dinsa daga
mmcstore izuwa mmcstore.txt kunga
kun qara .txt kenan
5. Daga nan zaka iya ganin Password din
memory card din da ka manta a baya,
saika rubuta wato kayi Copy dinsa
6. Saikaje kan Memory Card din ka danna
Option saika shiga remove Memory
Card Password, saika yi Paste din
Password din daka riga ka Copy.
Shikenan Ka Kammala.
Da fatan kunji dadin wannan darasi....
karku manta sharing da abokanku.

Drop Your Comment

0 Comments